Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Wata 'Yar Shekaru 4 Daga Ukubar Mahaifinta Da Matarsa


Rundunar ‘yan Sandan jihar Bayelsa, ta ceto wata yarinya mai skekaru hudu daga ukubar mahaifinta da matar shi.

Mahaifin wanna yarinya da matarsa sun dade suna ganawa wannan yarinya mai shekaru hudu azaba wai domin kawai tana fitsari a kwance.

Amma da Allah yayi cewa dubu ta cika sai suka kona ta da irin abinda ake tafasa ruwa yayi zafi, sai da kafen yayi ja sai suka nana mata a jiki.

Ganin haka yasa wasu makwabta suka kai batun ga hukumar ‘yan Sanda, su kuwa basuyi kasa a guiwa ba suka nufi gidan suka damke miji da mata.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Bayelsa, Asinim Butswat, yace ana ci gaba da bincike akan lamari, ita kuwa yarinya da ta sami kuna mai tsanani tana asibiti inda akeyi mata magani.

XS
SM
MD
LG