Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Alamun Korea Ta Arewa Nada Hannu A Kutsen "Ransomware"


Jiya Litinin masu binciken harkokin tsaron hanyar sadarwar internet suka ce akwai alamun Koriya ta Arewa tana da hannu a kutsen komfutocin da aka yi.

Kamfanonin Symantec da na Kaspersky dukkansu sun ambaci wata dabara da aka taba amfani da ita a lokutan baya, da ake kira Lazarus Group da tayi sanadin kutsen da aka yiwa kamfanin fina finai na Sony da ya shafi wadansu fitattu a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, wanda aka dorawa Koriya ta Arewa alhaki.

Sai dai kamfanonin tsaron sun ce za a yi riga mallam masallaci idan aka yanke hukumci nan da nan, saboda mai yiwuwa ne wani ne ya kofi hanyar kutsen domin yin amfani dashi a wannan lokacin da ake ciki.

Da alama, an sami dan sarari a kutsen kwamfutocin da aka kai a kasashen dabam dabam na duniya jiya Litinin, ko da yake an kaiwa dubban kwamfutoci, galibi a yankin Asia hari, lokacin da mutane suka isa bakin aiki, a karon farko tunda manhajar dake cutar da comfutoci ta bazu a kasashe dari da hamsin kwanaki uku da suka shige.

Jami’an lafiya a Birtaniya, inda kutsen ya gurguntar da ayyukan jinya da suka hada da fida da ganin likita, sun ci gaba da fuskantar matsala jiya Litini. Sai dai ministan lafiya na kasar Jeremy Hunt yace, an yi sa’a ba a sake kai wani hari na biyu ba.

A Amurka, Tom Bossert, mai ba shugaba Trump shawarwari kan harkokin tsaron cikin gida, ya shaidawa tashar ABC cewa, kawo yanzu, sun shawo kan kutsen komfutar da ya kawo cikas a kasashe da dama na duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00

XS
SM
MD
LG