Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ajax Zata Kara Da Manchester United A Europa League Final


Kungiyar kwallon kafa ta Manchester tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Celta Vigo, ta kasar Spain a gasar cin kofin Turai Europa League, na shekarar 2016/17 a karawarsu ta biyu, inda a haduwarsu ta farko Manchester ta doke Celta Vigo a gidanta da kwallo daya mai ban haushi wannan yabada Manchester United jimilan kwallaye 2 Ita kuma Celta vigo tana da 1.

Sakamakon wannan nasara da Manchester tayi, ya bata damar zuwa wasan karshe na cin kofin Turai Europa league 2016/17.

Zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Ajax wacce ta samu nasarar kaiwa ga wasan karshe sakamakon wasan da sukayi da Lyon a wasan dab da na karshe inda Lyon ta shata 3-1 a zagaye na biyu sai dai tun karawarsu ta farko Ajax, ta samu nasarar doke Lyon, da kwallaye 4-1, Hakan ya ba Ajax dama tana da kwallaye 5 ita kuma Lyon 4.

Za'a buga wasan karshenne ranar laraba 24 ga watan Mayu 2017, a Friend Arena Stockholm.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:13 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG