Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adana Kayayyakin Tarihi da Aladu Abun ne mai Mahimmanci


Gidan Makama, Kano
Gidan Makama, Kano

Adana kayayyakin tarihi da aladu abun ne dake bayana asali ko mutune, ko ya kan tunatar akan wani abun mai mahimmaci da ya faru a baya, Tare da bayana aladun iyaye, da kakanni.

Ginin ganuwa da kofofin Kano abun tarihi ne da jihar Kano ke alfahari dashi.

Tarihi ya nuna cewa an fara gina ganuwa Kano tun lokacin Sarki Giji, tsakanin shekarun 1095 zuwa 1133 aka kuma kamalashi a tsakiyar karni na sha hudu, lokacin Sarki, Zamnagawa, aka kuma shiga bunkasata a karni na sha shida.

Ganuwa na tai makawa wajen sa ido wajen shige ta fuje a birnin Kano.

Shugaban sashen tarihi na Jami’ar Bayeru dake kano, Dr, Ibrahim Khalil Abdulsamad, yace ginin ganuwa da kofofin Kano yana da mahimmanci sosai kasancewar ababen tarihi a Afirka, kuma inda har aka rasasu akwai wahala wajen maida gurbin su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG