Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Ajax Da Manchester United Zasu Buga Wasan Karshe Na Europa


A yayin da aka kammala lig lig na wasu kasashe musanman nahiyar turai yanzu hankali ya karkata wajan wasan karshene na cin kofin nahiyar turai wato Europa League na shekara 2016/17

Inda a yau za'a buga tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Ajax dake Netherlands da Manchester United na kasar Ingila

Saidai manyan 'yan wasan Manchester united irin su Zlatan Ibrahimovic, da Marco Rojo, ba zasu samu damar fafata wannan wasanba sakamakon jinya da sukeyi.
Shima mai tsaron gida na Manchester United, Eric Bailly ba zai fafata ba sakamakon Jan kati da alkalin wasa ya bashi a wasan da Manchester tayi da Celta Vigo, a gasar ta Europa na bana a wasan dab da karshe wanda United ta ci Celta 2-1

Kungiyoyin dai sau ukku suna fafatawa a tsakaninsu tun bayan kahuwarsu
Manchester united tayi nasara sau daya Itama Ajax sau daya anyi kunnen doki sau daya

Duk kungiyar da tayi nasara a wasan na yau zata samu tikitin zuwa gasar cin kofin zakarun turai na 2017/18


Za'a buga wasan na yau a filin wasa na Friends Arena mai daukar mutane dubu hamsin dake kasar Sweden da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG