Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekaru 70 Bayan Mutuwar Tsohon Sarki, Gawar Shi Ta Tada Zaune Tsaye


Sarki Victor Emmanuel na III
Sarki Victor Emmanuel na III

Bayan shekaru 70, da mutuwar tsohon sarkin kasar Italiya Victor Emmanuel III, wanda yayi gudun hijira daga kasar zuwa kasar Misira, a karon farko an maida gawar tashi kasar Italiya don yimi shi jana’iza, a kasar shi ta haihuwa.

Daga isar gawar tashi ta tada kura, domin kuwa ta tunama wasu daga cikin mutane da su kayi zamani da shi, wasu abubuwa da suka faru da har su kayi sanadiyar gudun hijirar tashi.

Ana dai yima sarkin kirari da “Kaifi Daya” saboda irin akidar shi, kuma mutun ne da bashi da tsawo amma sai fitina, sabo da irin rashin tsawon shi, sai da aka kera mishi takobi na musamman, wanda yayi dai-dai da tsawon shi.

Mutun ne da yayi sarauta da ta taba rayuwar mutanen Italiya a wancan lokacin, mutun ne da yayi yaki da tsarin gurguzu, da cin amanar ‘yan kasa da masarauta keyi a wancan lokacin.

Kimanin karni na 7 kenan da mutuwar shi, amma a yau irin akidojin shi suna tada zaune tsaye a kasar ta Italiya, ya mutu a kasar Masar a shekarar 1947, wanda ya bar kasar shi sabo da tsoron sojojin kasar Jamani. Biyo bayan karya yarjejeniyar tsagaita wuta, a lokacin yakin duniya na biyu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG