Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashiya 'Swetha' Ta Dau Alwashin Ilmantar Da Kananan Yara Harshen Kwamfuta


Swetha Prabakaran
Swetha Prabakaran

Ilimin sarrafa na’urar kwamfuta ba a kasar Amurka, kadai yake ilimi da akafi samun kudi akan shiba. Ganin yadda duniya take kara zama karamin kauye, ko zaure daya. Dalibai da yawa a kasar Amurka musamman a matakin firamari, basu samun damar daukar darusa da suka hada da ilimin kwamfuta.

Hakan yasa wata matashiya Swetha Prabakaran, daukar azama wajen ganin ta koyar da yara dake matakin makarantun firamari ilimin sarrafa kwamfta. Da’ake ma lakani da ‘Computer Coding’ itace hanya daya da ake bi don zayyana ma kwamfuta abubuwan da zatayi a lokacin da ake bukata.

Matashiyar Swetha, 'yar makarantar sakandire aji 3, a makarantar koyon ilimin kimiyya da fasaha, dake jihar Virginia a kasar Amurka. Ta assasa wata kungiya da take aikin ilmantar da yara ilimin kwanfuta ba kawai a kasar Amurka ba, har ma da sauran kasashe afadin duniya.

Kungiyar mai suna kowa zai iya kirkirar manhajar kwamfuta ‘Everybody Code Now’ a turance. Yanzu haka suna yunkurin hadin gwiwa da wasu kasashe kamar su India, Ghana, da makamantan su, baya ga wasu jihohin Amurka.

Don ganin sun fito da wata hanya da za’a koyar da yara, tun daga matakin firamari ilimin sarrafa kwamfuta. Matashiyar ta bayyanar da cewar “Gaskiya samun ilimin kwamfuta tun mutun yana yaro, ba karamar damace ba, da zata buda ma yara kwakwalwar su matuka, tun kamun girma”

Ta bayyanar da hakan ne a yayin wani taron ilimantar da yara da su kayi, a babban birnin tarayyar Amurka. Wanda aka gudanar ma yara 'yan shekaru 5, 6 7. Tana ganin cewar, kwakwalwar yara na budewa don fahimtar karatu, idan suna da wayewar sanin lungu da sako na kwamfuta.

A shekarar dai da ta gabata ne, aka karrama wannan matashiyar ‘yar sakandire a fadar shugaban kasar Amurka. A matsayin mace mai kokarin bada gudun mawa wajen ciyar da kasa gaba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG