Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Kwallon Kafa Lionel Messi Ya Zama Angon Antonell


Ango Lionel Messi da amaryar shi Antonell Roccuzzo
Ango Lionel Messi da amaryar shi Antonell Roccuzzo

Shahararren dan wasan kwallon duniya Lionel Messi, ya auri tsohuwar budurwar shi, kuma uwar 'yayan shi Antonell Roccuzzo. Itace budurwar shi ta farko tun yarinta, a ranar Asabar da ta gabata ne, aka daura auren su.

Messi da amaryar shi, sun kwashe tsawon lokaci tare da abokai da masoya a wani filin shakatawa suna wasannin nishadantarwa. Sun fara soyayyar su tun a shekarar 2008, amma sun san juna tun suna ‘yan shekaru 5.

Bukin nasu ya dau hankali matuka a kasar ta Argentina, wanda baki daga koina suka halarta, mawakiya Shakira, na daya daga cikin manyan baki a ranar bukin.

‘Ya’yan su biyu Thiago da Mateo, suna daga cikin mahalarta shagugulan bukin. Sai a ranar bukin ne suka bayyana ma jama’a wani rubutun alkawali da sukayi a jikin su, wanda yake nuna alkawalin ranar auren su da alamar kara dankon soyayya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG