Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Ya Kai Damo Ga Harawa! Cin Naman Shanu Haramun Ne A Wata Alkarya


Naeem Rabbani, wani mai Otel a jihar Rajasthan ta kasar India, ya nuna damuwar shi matuka, biyo bayan rufe otel din shi, da hukumomi su kayi na tsawon makonni. A ranar Talata ne jami’an ‘yan sandar jihar suka tabbatar da cewar, sakamakon gwaji da akayi a wani nama da aka daukko daga Otel din Hayat Rabbani, cewar ba naman saniya bane.

Shanu a kasar, dabba ce da ake bauta mata, hakan yasa ba’a yanka shanu balle a ci naman. Shanu akan ajiye su ne don bauta musu, da rokon su sa’a. Ga mabiya addinin Hindu, haramun ne mutun yaci nama musamman na shanu. Akwai dokoki kwarara wanda suka hana yanka shanu a wasu jihohin kasar India.

A tabakin mai Otel din Naeem Rabbani, da farko na gayama mutane cewar, wannan ba naman shanu bane, naman kazane, amma babu wanda ya yarda dani, daga cikin jima’an gwamnati. Duk bayanan da aka fitar a jaridu bana gaskiya bane.

An rufe Otel din ne biyo bayan zanga-zanga da aka gudanar a bakin Otel din, wanda kungiyar ‘yan rajin kare hakkin shanu suka gudanar, jaridar ‘India Express’ sun ruwaito cewar daya daga cikin masu zanga-zangan na bayyanar da cewar suna wannan zanga-zangar ne biyo bayan labari da suka samu.

Na cewar ana bukin faty, an yanka shanu a wannan otel din kuma an ci, sun samu sakon ne daga shafin WhatsApp, wanda ake zargin shugaban karamar hukumar Jaipur ya aika.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG