Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Zasu Dauki Karin Ma'aikata 3,000 A Fadin Duniya


Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg
Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg

Shafin zumunta na Facebook, na wani yunkuri don magance matsalolin da ake cigaba da fuskanta a fadin duniya, da suka shafi labaran kanzon kurege, bidiyon kashe-kashe, aikin ta’addanci, dai duk wasu bidiyo da kan iya zama hanyar nuna rashin da’a.

A jawabin shugaban kamfanin Mr. Marck, lokacin rufe wani taro da kamfanin suka shirya mai take F8, don zakulo matasa masu hazaka. Kamfanin yana shirin daukar karin matasa 3,000 a fadin duniya, wanda aikin su duba da tantance duk wani bidiyo da aka daura a shafin, kana da cire duk wani bidiyo da ke dauke da wasu abubuwa da basu dace ba.

Kamfanin dai na cigaba da fuskantar matsin lamba, dangane da damar da suka ba ma mutane su dinga daura bidiyo a shafufukan su. Duk dai da cewar dokokin shafin shine, babu wani bidiyo da za’a saka mai dauke da wasu labarai da suka keta hakkin bil’adama.

A jiya Laraba, ne shugaban kamfanin ya bayyanar da daukar karin matasan, don kara azama da wannan yakin, inda zasu kara yawan ma’aikatan kari da 4,500 da suke dasu. Ya kara da cewar, kamfanin zasu inganta na’urorin su don tantance duk wani bidiyo da mutane suka daura kamin su shiga duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG