Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mata Ba-Ingila Ta Dauki Juna Biyu, Sau Biyu A Lokaci Daya


Jarirai 'Yan Uku
Jarirai 'Yan Uku

Wata mata ‘yar asalin kasar Birtaniya, ta shiga cikin tarihin duniya, inda ta samu juna biyu, bayan sati biyu kuwa sai ta sake samun wani juna biyu, ana kiran wannan baiwar a turance ‘Superfoetation’ wani yanayi da mace kan dauki ciki sau biyu wanda ba kasafai hakan ke faruwa ba.

Wannan wata baiwa ce da Allah, kanyi ma wasu kadan daga cikin mutane, ita dai wannan matar ta samu cikin tagwaye, bayan sati biyu kuma sai wani cikin ya sake shiga, inda ta samu karin da a cikin cikin ta.

Ta haifi ‘yan uku. Masana sun bayyanar da wannan a matsayin wani abu da bai cika faruwa ba, a cikin kimanin shekaru 100, da suka wuce, wannan matar itace mace ta shida, da ta samu daukar ciki biyu a lokaci daya.

A cewar Farfesan lafiya Simon Fishel “Hakan bai kamata ya faru ba, amma gashi ya kasance” tun a shekarar 1865, aka fara ganin irin wannan abun, tun daga lokacin kuwa zuwa yau an samu mata shida da suka tsinci kansu a hakan.

Ya kara da cewar, dukkan mu mun dauka idan mace ta samu juna biyu shike nan, amma a shekarar 1978, wani likita da ya karbi wata haihuwa mai kamar hakan, ya kara tabbatar da hakan na aukuwan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG