Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tauraruwar Matashin Mawaki Justin Bieber, Na Neman Ragewa!


Matashin Mawaki Justin Bieber.
Matashin Mawaki Justin Bieber.

Biyo bayan wani taron masoya da aka gabatar, a bakin wani katafaren otel da ya sauka, shahararren matashin mawakin Amurka Justin Bieber, ya kara nuna mugun halin shi na kin magana da masoyan shi.

Wata matashiya masoyiyar shi ta bukaci da su dauki hoto, amma ya kiyarda da hakan, wanda har ya maida mata da bakar magana. Inda yake cewa ki dubi matakin girmamawar ki. Wannan wani mugun hali ne da aka san matashin mawakin da shi.

Matashiyar ta roke shi da cewar tana son yin hoto da shi, amma bai aminta ba, wannan bashi ne karo na farko da yayima masoyan shi haka ba, mussamman ‘yan-mata.

Matashiyar Sebah Helal, mai shekaru ashirin 20, tace gaskiya abun da yayi mata shine cin zarafi na karshe, domin kuwa har mahaifiyar ta na gaya mata cewar, ya wulakanta ta. Bayan kwashe awowi suna jiran shi ya fito, daga otel din shi amma yana fitowa sai yayi musu wulakanci.

A ‘yan watanin baya mawakin ya bayyanar a shafin shi na instagram da cewar, kada wani masoyin shi ya sake ganin shi a kan hanya yace yana bukatar daukar hoto da shi, don ya gama daukar hoto da mutane.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG