Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin FA Cup 2016/2017


A cigaba da wasannin FA Cup 2016/2017 wanda akeyi a kasar Ingila Jiya kungirar kwallon kafa ta AFC Wimbledon tasha kashi a hannun Sutton United daci 3-1

Fleetwood ta samu nasara akan Bristol City da ci 2-0

Burnley ta lallasa Sunderland da kwallaye 2-0

Crystal palace nada 2 Bolton W nada 1

Lincoln ta casa lpswich Town da ci 1-0

A yau kuma za'a cigaba da karawa a Sauran wasannin na FA Cup inda kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United, zata kece raini da Birmingham City, Plymouth kuwa zata fafata da Liverpool.

Ita kuwa kungirar kwallon kafa ta Southampton, zata gwabza da Norwich City da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.

A can kasar Spain kuwa a yau za'a kece raini a bangaren Copa del rey 2016/2017 a wasan kusa da na kusa da na karshe (Quater Final) Kungirar kwallon kafa ta Alcorcon zata karbi bakuncin Alaves, Real Madrid zata fafata da Celta Vigo

Za'a buga wasannin a lokota daban daban tun daga karfe bakwai da kwata na dare harzuwa karfe tara da kwata agogon Najeriya da Nijar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG