Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Messi da Ronaldo Zasu Fafata a El-clasico 2016


Gobe Asabar 3/12/2016 za'a kece raini a babban wasan kwallon kafa Mai taken El-clasico 2016, bangaren La-liga na shekara 2016/2017 na kasar Spain mako na goma sha hudu, tsakanin manya Kungiyoyin kwallon kafa na kasar wato Barcelona da Real Madrid.

Kowace kungiya ta shirya domin tunkarar wasan Shahararrun ‘yan wasan kwallon kafa a duniya, Lionel Messi, na Barcelona da takwaransa Cristiano Ronaldo, na Real Madrid, zasu haskaka a wasan.

Miliyoyin masu sha'awar kwallon Kafa ne zasu kashe kwarkwatar idanunsu wajan kallon wannan babban wasa.

Shi dai wannan wasa ana yinsa ne aduk shekara sau biyu a bangaren La-liga, inda kowace kugiya take zuwa gidan kowa domin fafatawa.

A shekarar da ta gabata 2015/2016 Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tabi Real Madrid, har Bernabeu, ta shata 4-0 daga bisani Real, ta bi Barcelona, Camp Nou, itama ta samu nasara 2-1.

A wannan karon Kungiyar Barcelona, ne zata karbi bakuncin Real Madrid a Camp Nou a gobe 3/12/2016 da misalin karfe hudu da kwata na yamma agogon Najeriya Nijar da kamaru.

Za'a sake gwabza karo na biyu ranar 22/4/2017 a gidan Real Madrid a lokacin ana mako na 33 a gasar La-liga 2016/2017.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG