Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon wasannin Copa Del Rey 2016/2017


A jiya aka buga wasan cin kofin Copa del rey, na shekarar 2016/2017 a kasar Spain inda kungiyoyi suka kece raini a tsakaninsu Kungiyar kwallon kafa ta Real Valladolid ta sha kashi a hannun Real Sociedad daci 3-1.

Huesca ta yi canjaras 2-2 tsakaninta da Las Palmas.

Gimnastic Tarragona, bata ji da dadiba a hannun Alaves da kwallaye 3-0

Racing nada 1 sevilla nada 2.

A kasar Ingila kuwa Gobe idan Allah ya kaimu za'a dawo cigaba da wasannin firimiya lig na shekarar 2016/2017, mako na goma sha hudu

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, zata karbi bakuncin Chelsea,

Sunderland kuwa zata kara da Leicester City, Stoke city zasu kece raini da Burnley, Crystal Palace da Southampton, Westbromwich da Watford

Tottenham zasu marafci Swansea.

Daga karshe Kungiyar Westham zasu fafata da takwaranta ta Arsenal

Za'ayi wasanninne alokota daban daban agogon Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00


  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG