Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shirin Film Mai Taken "Dear Zindagi" Ya Mamayi 'Yan Kallo Da Masu Fashin Baki


Sabon Shirin film mai taken "Dear Zindagi" ya mamayi ‘Yan kallo da kuma masu fashin baki a kan harkokin fina finan Bollywood,mussanma masu sa’ido ta wajen Kasuwancin masana'antar Bollywood.

Gauri Shinde, ita ta bada umarnin Film din Dear Zindagi wanda shahararren Jarumi Shah Rukh Khan, ya fito a ciki tare da Jaruma Alia Bhatt, ya kuma fita a cinimomi a ranar Juma’a da ta gabata.

Labarin Film din da aka gina shi akan rayuwar wata yarinya da ke neman fahimta ko kuma sanin kanta ya sami cikakkiyar nasara daga 'yan kallo har da masu fashin baki.

Mujallar Times ta India ta bayyana cewa shirin madubi ne na rayuwa da ya zo da banbanci da jaruma Ali Bhatt, ta nuna da kuma gwaninta irin wadda akasan Shah Rukh Khan, da ita.

Shirin film din dai ba’a kasha masa kudi masu yawa ba amma sakamakon kyawun labarin da kuma irin yadda aka tsara sakin sa a cinemomi masu kallo zasu yi ta tururuwa zuwa kallon film din a wannan makon.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:58 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG