Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Fara Wakar Soyayya Domin Duniya Ta Sanni -Inji Mustapha Mazika


Mustapha Mazika
Mustapha Mazika

Na koma wakokin soyayya ne domin wakokina su sami shiga a masana’antar Kannywood, ko dan ta hakan al’umma da dama zasu san waye Mustapha Mazika.

Mustapha Mazika dai ya ce a farko iyayensa basu hana shi sana’ar waka ba, illa kalubalen daga fannin 'yan uwa ya fito, a ganinsu bai dauki turbar da ta dace ba suka kuma koka, ko da yake yace yau da gobe ta fi wasa da fadakar da su sannu a hankali sun gane cewa sana’a ce.

Ya ce ya fara waka ne tun lokacin da yake makarantar islamiyya inda ya faro da wakoki na kasida.

Mazika, ya ce kafin ya karkata ga tsintsar wakokin soyayya yana wakar 'yan biki, da siyaya da ma harkokin yau da kullum na rayuwa.

Mustapha Mazika,ya ce abu daya daga cikin abubuwan da suka hassasa fara wakarsa kamar burin kowanne mawaki dai bai wuce ya fadakar da al’umma ta hanyar nishadi da kuma ilmantarwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG