Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashin Mawaki "Justin Bieber" Ya Yarda Mic A Saman Stage!


Justine bieber
Justine bieber

Shahararren mawakin kasar Amurka, dan shekaru ashirin da biyu 22, “Justin Bieber” ya fusata kwarai da irin tarbo da masoyan shi su kayi mishi, yayin da yake gabatar da waka a birnin Manchester, dake kasar Ingila.

Mawakin yana cikin waka, ya sarara don gabatar dawa masoyan shi sakon kauna, sai filin ya dauke da ihu, hakan ya harzuka shi wanda ya kai shi ga sauka daga saman tubalin waka. Wani mashahurin abu da yayi shine, na yadda “Mic” wato amsa kuwa, domin kuwa hakan ya nuna irin fushi da yayi da irin ihu da mutane ke yimi shi.

Mawakin ya roki masoyan shi da cewar “Zaku iya yimun alfarma? Ku kwantar da hankalin ku na dan lokaci kadan, kada ku damu ai gani a gaban ku” ya cigaba da cewar, ai duk ina jinku, kuma kamata yayi ku nuna kaunar ku a cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Daga bisani ya amsa ma masoyan shi da wasu zafafan kalamu, wanda hakan yana iya zama sanadiyar wasu masoyan shi, su nesanta kansu da shi. Don ko a watannin baya, mawakin ya bayyanar da rashin jin dadin shi da yadda yake daukar hotuna da masoyan shi, hakan yasa yayi furucin cewar bazai sake daukar hoto da kowa ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG