Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Matan Zamani: Yawaita Shafe-Shafe Kan Nakasa Fata!


Kwalliyar 'Yan mata!
Kwalliyar 'Yan mata!

Kwararru na fuskantar matsalolin sace-sacen basira, wanda hakan yake maida mafi akasarin sana’o’i baya. Dabi’u irin na wasu bata gari na maida sana’o’i baya, da saka mutane cikin hadari cikin rashin sani.

Bincike da aka gudanar akan wasu masana gyaran fuskokin sanannun ‘yan mata fitattu, sun bayyanar da wani sakamako mai ban tsoro. Hanyoyi da mata a wannan zamanin kan bi, wajen kokarin gyaran fuskokin su ko jiki, da shafe-shafen wasu sinadarai, na jefa su cikin matsaloli da illar hakan zai bayyana a gaba.

“Yan mata kanyi amfani da wani nau’in man shafawa a fuska, da ya kanfi karfin fatar su, ko su shafa mai wanda yake busar da fata, duk a cikin neman burge samari ko kawaye. Kana yanayin wuri, idan akwai hayaki na iya cutar da fatar su, idan suka sa wasu manshafawar da yafi karfin fuskar ta su.

Haka da yawa ‘yan mata kan shafa wani nau’in mai a kasan idon su, wanda da yawa wannan man, yana da matukar illa ga kwayar idon mata, saboda wasu sinadarai da akayi amfani da su wajen hade-haden man. Haka ma da yawa ‘yan mata basa wanke fuskokin su, kamin shafa wadannan man, wanda idan akwai wata cuta zata iya zama kasan man, daga nan shine akan samu cutar kansar fata.

A karshe, sun kara da jawo hankalin ‘yan mata, da su yi taka tsan-tsan da irin man da suke shafawa a fuskokin su, da kokarin karanta sinadaran da akayi amfani da su wajen hada man, haka suyi amfani da ire-iren wadannan man a lokacin da suke da bukata ba kowane lokaci ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG