A cikin jerin abubuwan da suke kara kayatar da anguwa, gari, ko kasa shine tsarin gidaje. Kwararrun masana harkar zanen gidaje na duniya, sun zabi wasu ginanuwa a fadin duniya don bayyanar dasu a matsayin ginanuwa da su kafi kyau a fadin duniya.
Ginin Parthenon, a kasar Greece, na daya daga cikin ginanuwa masu kyau a duniya, sai ginin “National Congress of Brazil” na biye, kana dakin tarihi na “Sao Paulo” duk a kasar ta Brazil. Haka dakin bauta na Forbidden Temple, a garin Beijing kasar China, na cikin jerin gini da akayi ittifakin yana da kyau.
Haka shima ginin makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Florida a nan kasar Amurka, na cikin sahu, ginin Hubertus, da yake Amsterdam, a kasar Netherlands, shima ya ciri tuta wajen kayatarwa. Ginin Empire dake babban birnin New York, ya shiga cikin jeri, haka dakin bauta na Osaka, a kasar Japan, shima ya hadu. Hakama babban otel din da yafi tsawo a duniya na kasar Dubai ya shiga sahu.
Dakin karatu Enterprise na jami’ar East Anglia, a kasar Ingina shima yana daga cikin ginanuwa masu kyau a fadin duniya, sai dakin tarihi na Kimbell, a jihar Texas ta kasar Amurka. Shi kuwa ginin dakin kayan tarihi na Barnes dake birnin Philadelphia, a kasar Amurka ba’a barshi a baya ba, haka ginin Notre Dame Du Haut, a kasar France, yaci tuta wajen kawa, haka filin tashin jiragen sama na marigayi tsohon shugaban kasar Amurka John F. Kenedy, ya samu lambar zama cikin jerin ginanuwa masu kyau a fadin duniya.