Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo Ya Zama Zakaran Nahiyar Turai


Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo

Hukumar UEFA, ta fidda sunsn shahararren dan wasan kwallon kafa na Portugal mai taka leda a kunhiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo, a matsayin zakaran kwallon kafa na nahiyar yankin turai na shekaran 2016.

Shi dai Ronaldo, ya sami nasara ne akan takwarorinsa Anthony Gris man, dan kasar Faransa mai taka leda a Atletico Madrid, da Garry Bell, dan kasar Walesm mai bugawa Real Madrid.

Kungiyoyin ‘yan jarida bangaren wasan kwallon kafa na duniya su suka yi wannan zabi, wannan shine karo na biyu da Cristiano Ronaldo na rike wannan matsayi, inda ya rike a shekara ta 2013 zuwa 2014.

A yanzu haka ya kamo Lionel Messi, wanda shima sau biyu ya rike wannan matsayi. Ronaldo, ya sami nasara ne a bisa hazakar shin a taimakawa kungiyar Real Madrid, inda ta sami nasarar cin kofin champions lig, na bana, yayin da ya sake jagorancin kungiyar kwallon kafa ta kasar sai wato Portugal, suka sami nasarar lashe gasar kasashen nahiyar Turai, da aka kammala a kasar Faransa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

XS
SM
MD
LG