Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UEFA Ta Fitar Da Tsarin Rukunin Kungiyoyin Kwallon Kafa


Hukumar shirya gasar cin kofin Zakaru na nahiyar Turai UEFA, ta fitar da tsarin rukuni rukuni na kungiyoyin da zasu fafata a wasanin bana.

An dai fida rukuni takwas, inda na “A” keda Paris Saint Germain, daga kasar Faransa, sai Arsenal daga kasar Ingila, sai Basel daga kasar Sweden yayinda Ludogorets ta fito daga kasar Bulgaria.

A rukunin “B” kuwa Benfica daga kasar Portugal, sai Napoli daga kasar Italiya sai Dyanamo daga kasar Ukraine, sai Besiktas, daga kasar Turkiyya.

A rukunin “C” akwai Barcelona na kasar Spain, sai Manchester City, daga Ingila Borussia Mouch daga kasar Jamus sai Celtic daga kasar Scotland.

Rukuni “D” nada Bayern Munich daga kasar Jamus, Atletico daga kasar Spain, sai PSV, daga kasar Netherlands sai Rostov daga kasar Rasha.

Rukunin “E” akwai CSKA Moscow daga kasar Rasha, sai Bayer Leverkusen daga kasar Jamus, sai Tottenham daga kasar Ingila sai Monaco da ta fito daga Faransa.

A rukunin “F” kuma akwai Real Madrid, da ta fito daga Spain, sai Borrusia Dortmund daga Jamus, sporting Lisbon ta fito daga kasar Portugal Legia Warsaw da ta fito daga kasar Poland.

Rukunin “G” akwai Leicester City, ta fito daga kasar Ingila sai Porto daga kasar Portugal, sai club Brugge da ta fito daga kasar Belguim, yayin da København ta fito daga kasar Denmark.

Juventus, tana rukunin “H” ta fito daga kasar Italiya, Sevilla ta fito daga kasar Spain, sai Lyon daga kasar Faransa sai Dinamo Zagreb daga kasar Croatia.

Ranar 13, ga watan Satumba ake sa ran fara wasan inda ake sa ran kammala wasan a ranar 3, ga watan Yuni na shekara 2017.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG