Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Masu Karffin Tattalin Arziki A Fadin Duniya!


Dallar Amurka
Dallar Amurka
A wani bincike da aka gudanar da ya bayyanar da kasashe ashirin da biyar 25, da su kafi kudi a duniya, da yadda kasashen suka samu kudin su. Kasar farko itace kasar “Qatar” wadda take cikin daular kasashen larabawa. Kasar dai nada karfin tattalin arziki dake bayyanar da kwatankwacin kudin da kowanne dan kasar yake samu a shekara. A kasar dai da keda yawan mutane 2,172,065. Mutane na samun albashi daya kai dallar Amurka $139,760 dai-dai da naira 27,952,000 a shekara. Kana mutane kanyi rayuwa har na tsawon shekaru 79, kamun mutuwa. Baki daya a shekarar 2014 an kiyasta kasar na da karfin arziki GDP da ya kai dallar Amurka $211.8 Billiyan. Dai-dai naira tiriliyan 42,360,000,000,000 Karfin kudin su daga albarka mai ne wanda suke na 9, a duniya da sukafi kowace kasa yawan wajen ajiye mai.

Sai kasa ta biyu mai karfin arziki a duniya, itace kasar “Macao Sar, China” Kasar dai nada karfin tattalin arziki dake bayyanar da kwatankwacin kudin da kowane dan kasar yake samu a shekara. A kasar dai da keda yawan mutane 577,914. Mutane kansamu albashi daya kai dallar Amurka $118,110 dai-dai da naira 23,622,000 a shekara. Kana mutane kanyi rayuwa har na tsawon shekaru 80, kamun mutuwa. Baki daya a shekarar 2014 an kiyasta kasar na da karfin arziki GDP da ya kai dallar Amurka $55.5 Billiyan. Dai-dai da naira tirilliyan 11,100,000,000,000. Karfin kudin su daga ca-ca ne, inda ta zama babban birnin ca-ca a yankin kasashen Asia.

Kasa ta 3, da tafi kudi a duniya kuwa itace kasar “Kuwai” Kasar dai nada karfin tattalin arziki dake bayyanar da, kwatankwacin kudin da kowane dan kasar yake samu a shekara. A kasar dai da keda yawan mutane 3,753,121. Mutane kan samu albashi da ya kai dallar Amurka $82,210 dai-dai da naira 16,442,000 a shekara. Kana mutane kanyi rayuwa har na tsawon shekaru 75, kamun mutuwa. Baki daya a shekarar 2014 an kiyasta kasar na da karfin arziki GDP da ya kai dallar Amurka $175.8 Billiyan. Dai-dai da naira tirilliyan 35,160,000,000,000. kasar Kuwai, karfin kudin su daga arzikin mai ne.
  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG