Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Matasa Da Wasani Ya Ce An Sace Kudaden Ne


Ministan Matasa Da Wasanni Barista Solomon Dalung
Ministan Matasa Da Wasanni Barista Solomon Dalung

Ministan matasa da wasanni na Najeria Barrister Solomon Dalung, ya danganta rashin tabuka abin kirki a gasar Olympic, na wannan shekaran akansace kudaden da aka ware domin wani katafaren sansani domin ‘yan wasa da gwamnatin da ta shude tayi awon gaba da shi.

Ya ce wannan shine dalilin da yasa ma’aikatar matasa da wasani ta rasa kudade wanda hakkan ya shafi karancin kudi ga ‘yan was an da suka wakilci Najeriya, a gasar Olympic na b ana.

Dalung, da ya furta haka a wata hira da jaridar Punch, ya kara da cewa kudaden da aka ware domin gina sansanin horar da ‘yan was an domin kasancewarsu cikin kyakkawan yanayi nayi wasa a kow ane lokaci sun bace kafin ya kama aiki a matsayin Minista.

Yana mai cewa kudaden ba wai na kawata sansanin da kayayyaki horar da ‘yan wasa na zamni bane kawai har ma da na dauko kwararru domin horar da ‘yan wasan, amma a cewar ministan kudaden sun yi batar dabo.

XS
SM
MD
LG