Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Matashi Dan Najeriya A Ingila


 Theresa May
Theresa May

An sake kashe wani dan Najeriya, dan shekaru goma sha tara da haihuwa, mai suna Andre Aderemi, ranar talata da ta gabata a Ingila.

Shi dai wannan matashi, an ga wasu matasa dauke da makamai sun bishi a guje daga bisani suka cim masa suka ko soso keshi a unguwar Croydon a birnin London.

A cewar hukumar ‘yan Sandan birnin London, masu agajin gaggawa a fanin kiwon lafiya, sun garzaya wurin inda aka dauke shi a jirgin sama mai saukar ungulu zuwa asibiti inda daga bisani rai yayi halinsa.

Shi dai wannan matashin mayaki bincike ya nuna cewa abokin Fola Orebiyi, ne wanda shima aka kashe ranar 3, ga watan Yuli, na wannan shekara a unguwar Notting Hill, a London, da kuma Leoandro Osemeke, wanda aka fi sani da Showkey, wanda shima aka kashe ranar 5, ga wannan watan da muke ciki.

Duk matasan ukku da ake zargi da akata wannan ta’asa suna hannu in ji hukumar ‘yan Sandan.

XS
SM
MD
LG