Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tana Tara Samari Da 'Yan Mata Su Na Badala A Gidanta


Mutanen wata unguwa a birnin Kano sun tura kwamitin gyara kayanka na 'yan unguwar zuwa wani gida domin yin nasiha tare da jan kunnen wata matar da aka ce tana tara samari da 'yan mata a gidanta su na yin badala.

Amma kuma, an ce wannan mata ta wanke daya daga cikin 'yan kwamitin da mari, sannan ta bi wasu daga cikinsu har gida tana tuhumarsu da neman kuntata mata ko ci mata zarafi.

Matar dai ta ki yin magana a lokacin da wakiliyarmu ta nemi jin ta bakinta, amma sauran 'yan unguwar sun ce har yanzu ba ta daina ba, koda yake ta yi alkawarin kawo karshen wannan abu.

'Yan unguwar suka ce sun damu ne a saboda ganin ana yin shaye-shaye da wasu abubuwan da ba su kamata ba, abubuwan da ka iya bata sunan wannan unguwa tasu.

Ga cikakken bayani nan...

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG