Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Thierry Henry Yayi Ritaya Daga Yau Talata


Thierry Henry
Thierry Henry

A bayan da ya shafe shekaru 20 yana murza tamaula, shahararren dan wasan kasar Faransa, Thierry Henry, yace zai rataye takalmansa.

Yau talata Henry mai shekaru 37 da haihuwa ya bayyana yin ritaya daga buga kwallo a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana godiya ga masoyansa a saboda abinda ya bayyana zaman wannan gawurtacciyar tafiya.

Henry ya lashe kofin kwallon kafar duniya da kuma na nahiyar Turai tare da kungiyar kasarsa ta Faransa, kuma ana daukarsa a zaman mashahuran ‘yan wasan kwallon kafa na wannan zamani.

Thierry Henry ya sha ma kungiyar kwallon kafa ta Faransa kwallaye 51 a wasanni 123 da ya buga mata. Babu wani dan wasan Faransa da ya taba yin hakan.

Amma kuma Thierry Henry ya fi shahara a lokacin da yake wasa ma kungiyar Arsenal ta Ingila, inda ya jefa mata kwallaye har 228, abinda babu wanda ya taba yi mata. A wasannin lig na firimiya kawai ma kwallaye 175 ya jefa ma Arsenal.

A bayan nan, Henry ya shafe shekaru 3 a FC Barcelona kafin ya koma kungiyar New York Red Bulls ta Amurka inda daga nan yayi ritayar a yau talata.

An jima ana rade-radin cewa Henry na sha’awar zamowa kwach ko manaja na wata kungiya. A yanzu dai zai koma kasar Ingila inda zai zama mai fashin bakin kwallo ma gidan telebijin na Sky Sports.

XS
SM
MD
LG