Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Sojojin Burkina Faso Ya Dare Kan Mulki


Babban hafsan sojojin kasar Burkina Faso ya bada sanarwar cewa ya amshi ragamar mulkin kasar a bayan murabus din dadadden shugaba Blaise Compaore.

Janar Honore Traore ya fadawa 'yan jarida yau jumma'a a Ouagadougou, cewa ya "dauki nauyin shugabancin harkokin kasa."

Traore yace gwamnatinsa zata fara tattaunawa da dukkan bangarorin siyasar kasar ba tare da bata lokaci ba da nufin miado da "yin aiki da tsarin mulki."

Gidan telebijin na Burkina24 ya bada rahoton cewa tsohon shugaba Compaore ya fice daga fadar shugaban kasa a cikin wata kwambar motoci ta masu gadi dauke da manyan makamai.

Compaore ya shafe shekaru 27 yana mulkin kasar tun bayan da ya hambarar da uban gidansa Thomas Sankara a shekarar 1987.

XS
SM
MD
LG