Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Blaise Compaore Ya Sauka Daga Kujerar Shugabancin Burkina Faso


Blaise Compaore, tsohon shugaban Burkina Faso
Blaise Compaore, tsohon shugaban Burkina Faso

Rundunar sojojin Burkina Faso ta ce shugaba Blaise Compaore ya sauka daga kan karagar mulki, bayan da ya shafe shekaru 27 yana mulkin kasar.

Kafar labarai ta "Burkina 24 news" ta ambaci wani kakakin sojoji yana fadin cewa Compaore ya yi murabus yau jumma'a, kwana guda a bayan da 'yan zanga zanga suka cinna wuta a ginbin majalisar dokoki domin nuna rashin jin dadinsu da koikarin tsohon shugaban na sauya tsarin mulki da nufin yin tazarce.

Kakakin, Kanar Isaac Zida, bai fadi inda Mr. Compaore yake a yanzu ba, haka kuma bai bayyana wanda zai gaje shi ba.

Rabon da a ji wani abu kai tsaye daga Mr. Compaore tun jiya alhamis da dare, inda ya bada wata sanarwar cewa zai fara tattaunawa da 'yan adawa.

XS
SM
MD
LG