Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Koch din Tottenham a Shirye Yake don Magance Rashin Kokarin ‘yan Wasan shi


Sabon Koch din kungiyar kwallon kafa ta Tottenham yace a shirye yake don magance matsalar rashin kokarin ‘yan wasan shi. Alamu dai sun nuna cewar shike rike da ragamar shugabanci kungiyar, wanda kuma ya dau alwashin zai kawo ma Arewacin kasar Ingila kofufukan zinari.

Mr. Mauricio Pochettino, ba zaiyi mamaki da rashin kokarin da yan kungiyar Tottanham suka nuna a farkon wannan kakar ba.

A takaice ma ya hasashi irin wannan matsalar a lokacin da yake sa hannu a yarjejeniyar zama sabon shugaban kungiyar na shekaru 5, a ranin na shekara bara.

Mr. Pochettino, ya gayama babban shugana club din, Mr. Daniel Levy tun kamin ya iso cewar, za’a dauki watannin da dama kamin irin tsarinshi da kwarewarshi su ratsa jikin ‘yan wasan. Kamar yadda Mr. Brendan Rodger yake shugaban kungiyar Liverpool a karon farko a wannan kakar wasanin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG