Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Diego Costa Shi Ne Gwani A Watan Agusta A Ingila


Diego Costa na Chelsea yana murnar kwallon da ya jefa a ragar 'yan Leicester City a karawar Firimiya da suka yi a Stamford Bridge a watan Agusta.
Diego Costa na Chelsea yana murnar kwallon da ya jefa a ragar 'yan Leicester City a karawar Firimiya da suka yi a Stamford Bridge a watan Agusta.

A cikin shekaru goman da suka shige, ba a taba samun sabon dan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ya jefa kwallaye 4 a wasanni 3 na farko da ya buga ba.

Ya zamo sabon dan lelen magoya bayan kungiyar Chelsea, ba wai kawai don yawan kwallayen da yake jefawa ba, domin ganin yadda yake wasa da hankalin abokan karawar kungiyar, yana ba su haushi a cikin fili.

Kai, yawan kwallayen da ya jefa ma, fiye da rabin kungiyoyin dake bugawa a gasar Firimiya Lig ta Ingila har yanzu ba su jefa yawansu ba a raga.

Ana maganar Diego Costa ke nan, wanda Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta ayyana shi a zaman Dan Wasa Mafi Gwaninta a Wasannin Firimiya Lig na watan Agustan bana.

Costa, shi ne dan wasan Chelsea na fariko da ya lashe wannan kambi cikin kusan shekaru biyu. Dan wasan Chelsea na baya da ya samu wannan kambi shi ne Juan Mata, watanni 22 da suak shige, lokacin da ya zamo mafi gwanintan dan wasa na watan Oktobar 2012.

XS
SM
MD
LG