Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Lesotho Yana Afirka Ta Kudu Domin Tattauna Juyin Mulki


Firayim ministan Lesotho,Thomas Thabane
Firayim ministan Lesotho,Thomas Thabane

Firayim ministan 'yar karamar kasar nan ta Lesotho dake yankin kudancin Afirka, yayi tattaki zuwa kasar Afirka ta Kudu domin tattauna yamutsin da aka samu a kasarsa, abinda wasu suka bayyana a zaman yunkurin juyin mulki.

Thomas Thabane zai gana da shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma da kuma mukaddashin firayim ministan Lesotho, Mothetjoa Metsing, wanda Thabane yace shi ne ya kitsa wannan tashin hankalin.

An ji karar bindigogi jiya asabar a Maseru, babban birnin Lesotho. 'Yan bindigar da watakila sojojin kasar ne, sun kewaye gidan firayim ministan da wani babban jami'in 'yan sanda, suka kuma kwace makaman wasu caji ofis guda biyu na 'yan sanda.

Mr. Thabane ya bayyana wannan tashin hankali a zaman yunkurin juyin mulki, amma wani kakakin soja yace dakarun sun yi kokarin tabbatar da tsaron muhimman wurare ne kafin wani gagarumin gangamin nuna kin jinin gwamnati da aka shirya gudanarwa gobe litinin.

Jami'an sojan Lesotho sun ce sojojin sun kama cikin barikokinsu, kuma komai ya lafa a kasar.

XS
SM
MD
LG