WASHINGTON, DC —
Wata macen da aka bayyana ta da cewa karamar yarinya ce sosai ta tarwatse dazu laraba a ofishin gudanarwa na Kolejin Polytechnic ta Kano, ta kashe mutane 6 ta kuma raunata wasu guda 6.
Wannan shi ne karo na hudu da ake kai irin wannan harin kunar bakin wake a birnin na Kano cikin wannan makon.
An kai wannan harin a wata rumfar da aka kafa a kofar ofishin inda daliban da suka kammala karatun babbar diploma ta kasa, HND, suke duba sunayensu domin ganin inda aka tura su zuwa aikin bautar kasa.
Wasu majiyoyi sun bayyana wannan mace da cewa ba ta wuce yarinya 'yar makarantar firamare ba.