Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Philipp Lahm Yayi Ritaya Daga Kungiyar Kasar Jamus


Kyaftin na kungiyar kwallon kafar kasar Jamus, Philipp Lahm, yayi ritaya daga buga ma kasar kwallo. Yau Jumma’a Lahm mai shekaru 30 ya bayyana wannan ga shugaban hukumar kwallon kafar Jamus, Wolfgang Niersbach.

Lahm yace tun a farkon shekara yayi tunanin cewa zai yi ritaya daga buga ma kasar a bayan gasar cin kofin duniya, kuma ya bayyana farin cikin cewa kasarsa ce ta lashe kofin na duniya a wasansa na karshe ma Jamus.

Shugabannin kwallon kafa da ‘yan wasa a fadin duniya sun yi ta yaba ma Lahm, cikinsu har da shugaban hukumar FIFA, Sepp Blatter da shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel.

Lahm ya fara buga ma kasar Jamus wasa a 2004.

A kwanakin baya dai ya sake sabunta kwantarakinsa na buga ma kungiyar kwallon kafar Bayern Munich har zuwa shekarar 2018.

XS
SM
MD
LG