Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea Ta Sake Sayen Wani dan Wasan Atletico Madrid


Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sake sayen wani dan wasan kuma daga kungiyar Atletico Madrid, wannan karon Filipe Luis mai tsaron baya.

Sai dai Chelsea ta ce taransfa na Luis zai dogara ne a kan ko dan wasan mai shekaru 28 da haihuwa zai yarda da irin albashin da Chelsea zata biya shi.

Luis, dan kasar Brazil, shi ne zai maye gurbin tsohon dan wasan Chelsea Ashley Cole, wanda ya yi ban kwana da Stamford Bridge a lokacin da kwantarakinsa ya kare a karshen kakar kwallon da ta gabata.

Idan ba a manta ba dai, Chelsea ta riga ta raba Atletico Madrid da shahararren dan wasanta na gaba Diego Costa dan kasar Spain, wanda a jiya talata ya rattaba hannu kan kwantarakin shekaru biyar.

XS
SM
MD
LG